Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) Cikin Tafsirin Suratul Fatiha, aya ta 5–7: “Daga Imam Sadeeq (A.S), daga Imam Ali (A.S), ya ce: na ji Manzon Allah (S) yana cewa, Allah Azza wa Jalla ya ce: na raba Fatihatul-Kitab tsakanina da bawana rabi nawa, rabi nasa. Kuma duk abin da bawana ya tambaya zan ba shi.
Idan bawana ya ce: (بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ), Allah Azza wa Jalla sai ya ce: bawana ya fara da suna na, kuma tabbas ne a gare ni in cika masa duk al’amuransa, in sa masa albarka a duk abin da yake yi.
Idan bawa ya ce: (الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ), sai Allah Azza wa Jalla ya ce: bawana ya gode mini, ya kuma san ni’imar da yake da ita daga wajena ne, kuma ya san duk musifun da aka tunkuɗe masa ba su same shi ba; to da tagomashi na ne na tunkuɗe masa. Ina shaida muku, ya ku Mala’iku, ku sani zan gwama masa ni’imar duniyar nan da na ba shi ya gode, da kuma ni’imar lahira; zan tunkuɗe masa bala’o’in lahira kamar yadda na tunkuɗe masa na duniya.
Kun ga ni’imomin Allah guda biyu kenan: akwai ni’imar da ya ba ka, akwai ni’imar kare ka daga masifu duk shi yake yi. To in ka gode na nan, sai kuma Allah ya ba ka na can Aljanna kenan; ya tunkuɗe maka kuma na can wuta kenan.
Idan bawa ya ce: (الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ), sai Allah Ta’ala ya ce: bawana ya shaida cewa ni ne Ar-Rahman, Ar-Rahim. Na shaida muku, ya ku Mala’iku, zan cika masa kason sa, zan kuma cika masa rabonsa na ni’imata. Wato a nan lahira kenan.
In bawa ya ce: (مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ), sai Allah Ta’ala ya ce: ina shaida muku, ya ku Mala’iku, tunda ya yi i’tirafi da cewa ni ne ke da iko ranar sakamako, to zan sauƙaƙe masa hisabi a ranar, kuma zan nunnunka kyawawan ayyukansa, kuma zan ƙetara munanan ayyukansa.
Idan bawa ya ce: (إِيَّاكَ نَعْبُدُ), sai Allah Azza wa Jalla ya ce: bawana ya yi gaskiya, ni kaɗai yake bautawa. To ina shaida muku zan ba shi lada—ladan da duk wanda yake ibada ba irin yadda yake yi ba sai ya yi burin ya samu irin nasa.
Idan bawa ya ce: (وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ), sai Allah ya ce: wajena ya biɗi taimako, kuma ya nemi mafaka wajena ne. To ina shaida muku zan kiyaye shi daga al’amuransa, zan kuma taimake shi a kan dukkan wahaloli, kuma zan kama hannunsa a yayin da yake cikin wahaloli.
To idan bawa ya ce: (اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ) har izuwa ƙarshe (صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ), sai Allah Azza wa Jalla ya ce: wannan na bawana ne kenan. Ba ya ce ya raba biyu ba? To wannan na bawana ne. Na ba shi duk abin da ya roƙa, na amsa ma bawana, na kuma ba shi abin da yake buri, kuma na amintar da shi daga abin da yake tsoro.
To ka ga, idan bawa ya san ma’anar Fatihatul-Kitab, yana karantawa yana faɗa, Allah yana faɗa; ko yana faɗa, Mala’iku na ji. To Allah Ya sa muna cikin waɗanda Allah Ta’ala yake musu wannan.
@SZakzakysGallery
09/Ramadan/1447
26/February/2026
Your Comment